- Samu ƙarin bayani dangane da marubuciyar
- Game da kwanaki 16
- Game da Tasirin Asusun Kula da Harkokin Zamantakewar Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Etinosa Yvonne
Etinosa Yvonne (wadda aka haifa a shekarar 1989) ta kasance mai ɗaukar hoto na tarihi, sannan mai fasahar ɗaukar bidiyo ce wadda aka haifa kuma ta tashi a Nijeriya. Tana aiki da ma’aikatun fasaha da yaɗa labarai daban-dabam, ciki har da ɗaukar hoto da bidiyo.
Aikinta ya fi karkata kan bincike game da al’amuran da suka shafi yanayin da ɗan’Adam ke ciki da kuma adalcin zamantakewa. Etinosa na kallon aikin da take yi a matsayin wani abu da zai samar da sauyi a zamantakewar jama’a.
Haɗin guiwar da ta yi da hukumar UNFPA na tsawon kwanaki 16 kan Yin Allah-Wadai da Cin Zarafi da ya Shafi Jinsi (Nuwamba 25 — Disamba 10, 2020) ƙari ne kan shirinta da take gudanarwa mai taken Duk Yana Cikin Kaina, wanda ya shafi matakan da waɗanda suka tsira daga yanayin cin zarafi suke ɗauka wajen mancewa da abin da ya faru.
Ta hanyar Duk Yana Cikin Kaina, Etinosa na da zimmar kira ga samuwar tallafin masana lafiya ɓangaren ƙwaƙalwa (MHPSS) domin taimaka wa waɗanda suka kuɓuta daga halin cin zarafi.
Etinosa na ɗaya daga cikin fitattun masu basira guda shida da aka zaɓa a shekarar 2020 na shirin Hoton Jarida na Duniya 6x6 na masu fasahar Afirka. An nuna aikinta a ƙasashe daban-dabam na duniya sannan an wallafa su a ƙasashe daban-dabam da suka haɗa da BBC da The Guardian da Al-Jazeera.
Tun shekarar1991, daga 25 ga watan Nuwamba (wato Ranar Yaƙi don Kauda Cin Zarafin Jinsin Mata ta Duniya) har zuwa 10 ga Disamba (wato Ranar Kare Haƙƙin Bil-Adama), al’ummomi a duniya sun gudanar da juyayin kwanaki 16 na Gwagwarmayar Yaƙi Da Cin Zarafin Jinsin Bil-Adama.
A cikin shekarun da suka shude, kiraye-kirayen ofishin UNFPA da aka gudanar a lokutan Kwanaki 16 ya faɗakar da jama’a, tare da tattara kan masu kira da kuma fito a zahiri da ayyukan da aka ɗauka don yaƙi da nau’ukan cin zarafin jinsin bil-Adama kamar: cin zarafi ta hanyar neman yin lalata da kokarin aurar da yara ‘yan mata da wuri da yi musu kaciya da cin zarafin ma’aurata a tsakaninsu da kuma yin fyade da sauran miyagun dabi’o’i.
Duk da haka, wannan aiki bai tsaya ga kwanaki 16 kawai ba. Ofishin UNFPA na aiki a cikin ƙasashe sama da 130 don kokarin kawar da cin zarafi da kuma taimaka wa waɗanda suka kubuta daga cin zarafi, a kowace rana. A shekarar 2019, ofishin UNFPA ya samar da taimakon kiwon lafiya da na abin da ya shafi matsalar ƙwaƙwalwa ga mutane sama da 760,000 waɗanda kuma suka taɓa fuskantar cin zarafin jinsin bil-Adama. A daidai wannan lokacin, an gudanar da tsare-tsare da niyyar kawo ƙarshen matsalar aurar da yara ‘yan mata da wuri wanda adadinsa ya kai na ‘yan mata miliyan 2.5, kuma mata da ‘yan mata 300,000 da suka amfana daga tsare-tsaren a kokarin magance matsalar yi wa mata kaciya.
Tamkar yadda tsarin cin ma muradun ƙarni masu dorewa ya shata, ofishin UNFPA ya dukufa a kan ganin cewa ya kawo ƙarshen cin zarafin jinsin bil-Adama da sauran miyagun al’adu masu cutarwa daga nan zuwa shekara ta 2030.
Tun shekaru goma da suka shude, kungiyar maharan Boko Haram suka fara kai farmaki ga jama’a a arewa maso gabashin Nijeriya tana mai tursasawa miliyoyin mutane da tilas suka yi hijira daga gidajensu suka kuma nemi mafaka a sansanonin yan gudun hijira a cikin kasarsu. A matakin mayar da martani kuma da hada gwiwa da mutanen yankin da kuma Gwamnatin Nijeriya, ofishin UNFPA ya kakkafa cibiyoyi da sansanonin-na-tsira inda mata da matasa za su samu taimako da damar sake gina rayuwarsu da kuma samun magunguna game da inganta lafiyarsu daga bala’in da rutsa da su.
Tun lokacin da tashin hankali ya ɓarke, ofishin UNFPA ta samar da cibiyoyi a matsayin mafaka guda 37 a sassa daban-dabam na yankunan. Ofishin na ba da taimakon magunguna da damar ganin likita, musamman abin da ya shafi matsalar ƙwaƙwalwa da tunani (MHPSS); da kuma horaswa a kan sana’o’in dogaro da kai. Mahalarta sun koyi abubuwa da suka shafi kiwon lafiya, musamman a lokacin annobar COVID-19, haƙƙoƙin mata da kuma kiwon lafiyar da ya shafi matsalar haihuwa (SRH) kamar ba da tazarar iyali da kiyayewa da tsabta a lokutan haila. “Dukkan cibiyoyin da ake mafani da su a matsayin mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira da kuma al’ummar da suka ba su masauki, an samar musu da kaya don ba da taimakon kariya da kuma samar da muhalli mai kyau ga ‘yan gudun hijira don su samu walwala, su kuma sake inganta zamantakewarsu tare da samun kwanciyar hankali,” in ji Dr. Midala Usman Balami, wato ƙwararre a kan harakar tsare-tsare a ofishin UNFPA a jihar Borno. Ya kara da cewa, taimakon “Na rage raɗaɗi da damuwa a rayuwa.”
*Matan 16 da yan matan da suka fito a cikin wannan bincike mai taken “Muryoyin Da Ba A Ji Ba Daga Nijeriya,” wadanda kuma aka sakaya sunayensu saboda sirrintawa da lalurar tsaro, duka, a yanzu haka, suna ci gaba da karbar tallafi ne daga ofishin UNFPA a sansanonin da suke fakewa a ciki.
A faɗin duniya, cin zarafin mata na ɗaya daga cikin tauye hakkin ɗan’adam da ya fi ƙamari.
Danna nan don tsallake shafin gabatarwa
Kuna iya kuma duba shafua da ke kasa.
scroll down
04 Sep. 2019
Teen Vogue
23 July 2020
The Guardian
19 Nov. 2018
NBC Montana
04 June 2020
BBC News
01 Oct. 2020
CBS News
09 June 2020
Thomson Reuters
06 April 2020
UN News
A Nijeriya, kusan kashi 30 cikin ɗari na mata sun taɓa fuskantar matsalar cin zarafi da ya shafi jinsi
Nau’o’in farmaki da mayaka ke kai wa a Arewa-Maso Gabas a cikin shekaru goma da suka gabata, sun jefa mata da‘yan mata cikin masifar cin zarafin jinsi, a matsayin wani nau’in irin tashin hankali da ake fama da shi a yankin. Mata da ‘yan mata da gungun mayaka kan cafke, kan fuskaci matsalar fyaɗe ne da kuma auren tilas a yayin da suke shiga hannu. Idan kuma har suka yi sa’a suka kubuta, to suna kuma shiga karin matsalar kauracewa daga al’ummominsu. Wadanda suka samu damar kaucewa wannan tsangwama daga cikinsu kan fuskanci auren dole ne ko su sha duka a hannun mazajensu.
6 daga cikin mata 10
a Arewa-Maso-Gabashin Nijeriya sun ɗanɗani wasu nau'ukan cin zarafin jinsin bil-Adama (GBV)
6 daga cikin mata 10
women in northeastern Nigeria have experienced some form of gender-based violence (GBV)
53%
na 'yan gudun hijira (IDPs) da ke waɗannan jihohi duk mata ne da 'yan mata
miliyan 7.9
fiye da rabin mutanen wannan yankin ne ke neman agaji a shekara ta 2020
Idan sun yi nasarar kuɓuta, sukan shiga cikin karin yanayin tashin hankali, a lokacin da al'ummominsu suka kaurace musu. Dukkan matan da fitinu suka shafa, ko da kuwa sun kuɓuta daga hannayen 'yan garkuwa, sukan fuskanci shiga cikin karin haɗarin cin zarafin jinsin bil-Adama ne, kamar aure da wuri da duka a hannayen mazajensu