loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
0

Wannan labari  ya kasance amon murya ne na nau’o’in labaran mata da dama da ke fama da matsalar cin zarafi a gidajen aure a faɗin duniya. A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI: unfpa.org/unheardvoices/hadiza via @UNFPA #ENDviolence #16Days

https://www.unfpa.org/ha/unheardvoices/hadiza
Danna ka saurara

Mijina yana samun kuɗi wanda kuma ya ishe shi ya ciyar da ni da yarana gwargwadon hali. Na kasance ina sayar da lemon kwalba ina kuma amfani da kuɗin wajen tallafa wa iyali. Rayuwa ta kasance lafiya har zuwa ‘yan shekaru. A lokacin ne mahara suka kawo wa kauyenmu farmaki wanda hakan ya tilasta mana yin hijira.

Da ina jin daɗin kasancewa matar aure, amma ban da yanzu.

Daga baya, ya daina kawo komai gida. A maimakon haka, sai ya rinƙa satar abincin da nake samu daga ƙungiyoyi masu zaman kansu yana sayarwa, domin sayen abinda yakan sha. Idan na kuskura na yi masa magana, sai ya doke ni. Na rasa ƙimata. Yayin da nake tare da sauran mata, sai in rinƙa kallon su, amma ba na jin cewa ni mace ce

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Wannan labari  ya kasance amon murya ne na nau’o’in labaran mata da dama da ke fama da matsalar cin zarafi a gidajen aure a faɗin duniya.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne